Sufuri: Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Ranakun Tashin Jiragen Sama

Gwamnatin tarayya ta sanar da dawowar tashi da saukar jirage a wasu manyan filayen jiragen sama na kasar nan.

Ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika ne ya fitar sanarwar da yammacin jiya, inda ya ce jirage za su fara tashi da sauka a iya cikin gida Najeriya a Abuja, Legas, Kano, Fatakwal, Owerri da Maiduguri.

A cewar Hadi Sirika, jirage za su fara tashi a filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Legas da filin jirgin sama na Nmamdi Azikiwe da ke Abuja a ranar 8 ga watan Yuli, 2020.

Filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano da ke Kano da filin jirgin sama na Fatakwal a jihar Rives da na Maiduguri a jihar Borno za su fara aiki daga ranar 11 ga watan Yuli.

Sauran filayen jirgin sama na kasa zasu koma aiki daga ranar 15 ga watan Yuli, kamar yadda ministan ya bayyana.

Kazalika, Sirika ya ce za a sanar da ranar dawowar tashi da saukar jiragen kasa da kasa nan gaba, a karshe ministan ya bukaci jama’a su kara hakuri.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *