Ku Yi Hattara Da Boma-Bomai A Gonakinku – ‘Yan Sanda Sun Gargadi Manoman Yobe

Hukumar ‘yan sandan jihar Yobe ta shawarci manoman jihar Yobe da su yi hattara da abubuwa masu fashewa da aka binne a gonakinsu a yayin da suke gudanar da nomansu.

Wannnan gargadin ya fito ne daga bakin Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Dungus Abdulkarim a wata sanarwa da ya fitar a garin Damaturu.

Ya ce wannan gargadin ya zama wajibi ne duba da yadda irin wannan abu mai fashewa ya raunata wani manomi mai suna Adamu Haruna a garin Gujiba.

“Haruna ya tsinci wani abu ne mai fashewa a gonarsu, cikin rashin sani ya dauke shi zuwa gidansa. A yayin da yake kokarin bude shi, sai ya tashi da shi, inda ya yi masa mummunan raunuka a wurare daban-daban a jikinsa.” Inji Abdulkarim.

Ya kuma tabbatar da cewa; ‘yan sandan sun gano abubuwan masu fashewa (IEDs) a wadansu gonaki a garin Damaturu, da Buni Yadi bayan wannan lamarin ya auku. Inda ya sake amfani da wannan damar wajen gargadin manoman da cewa akwai yiwuwar Boko Haram ne suka binne boma-boman a kananan hukumomin Tarmuwa, Dapchi, Kanamma da Gulani dake jihar.

Abdulkarim ya shawarci manoman da su kai rahoton duk wani abu da suka gani ba su fahimce shi ba a gonakinsu zuwa ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa domin daukar matakai.

Har wala yau ‘yan sanda sun ce sun cafke wadansu mutum biyu da ake zarginsu da fashi mai suna; Garba Sale da Shehu Usman, a Dilawa dake karamar hukumar Geidam a jihar.

Abdulkarim ya ce wadanda ake zargi din su membobin wasu gungun mutum shida ne da suka addabi yankin.

Ana zarginsu da fasa gidan wani mutum mai suna Alhaji Adamu Jabure, inda suka yi yunkurin yi masa satar naira N900,000  a ranar 14 ga watan Yuni da misalin karfe 6 na safe. “Wadanda ake zargi din sun yiwa wanda suka je yiwa fashi barazanar da ya samar da kudin zuwa gobe kamar yadda ya yi alkawari.” Inji sanarwar ‘yan sandan.

Rundunar ‘yan sandan sun ce masu binciken kwakwaf na hukumar, tare da taimakon al’umma sun bi diddiginsu, inda har suka yi musayar wuta a Digare. “hudu daga cikinsu sun arce da raunuka a jikinsu daban-daban, a yayin da muka kama mutum biyu a yayin artabun.”

Abdulkarim ya ce daga cikin abubuwan da suka kwato daga hannun bata garin sun hada da bindigar AK 47, sai wasu harsasai masu rai guda 25 masu nisan mita 7.52, da kuma kwanson harsashin bindigar AK47 guda daya.

-Jaridar Madubi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *