KANO: Jami’an Karota Sun Kama Barasa Cikin A Daidaita Sahu

Hukumar kula da sufurin ababen hawa a jihar Kano (Karota) ta kama wani direban babur mai ‘kafa uku eanda ya dauko wani fasinja dauke da giya a cikin ‘katuwar jaka (Ghana most Go).

Tuni jami’an humumar Karota suka tisa ‘keyar direban babur din zuwa ofishin hukamar Karota don zurfafa bincike, inda suka mika giyar ga hukumar Hisbah ta Kano don gudanar da aiki akanta.

Shugaban hukumar Karota a Kano, Dr. Baffah Babba Dan Agundi ya yi kira ga direbobin babur mai kafa uku da su ‘kauracewa debo kayan laifi a baburan nasu domin inganta sana’ar tasu da kuma tsira da mutuncinsu, inda ya sha alwashin tabbatar da doka da oda akan titunan jihar Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *