Ilimi: Za a rarraba wa ɗaliban jihar Legas rediyo don daukar darussai daga gida

Gwamnatin jihar Legas ta ce ta na shirin rarraba rediyo 10,000 ga dalibai domin karatu daga gida.

Kwamishinar ilimi ta jihar Folashade Adefisayo ta ce jihar za ta yi hadin gwiwa da kamfanonin sadarwa wajen samar da intanet kyauta ga makarantu domin saukaka koyarwar ta intanet.

A ranar Litinin ne Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da sake bude makarantu ga daliban da ke ajin karshe a firamare da karama da kuma babbar sakandare domin ba su damar rubuta jarrabawar.

Sai dai sauran daliban da ba a ajin karshe suke ba za su ci gaba da zama a gida.

Gwamnatin ta Legas ta sanar da kudirin fara koyarwa ta rediyo domin tabbatar da cewa ba a bar daliban a baya ba a harkar karatunsu a wannan lokacin da ake fama da annobar korona.

Ms Adefisayo ta ce gwamnatin jihar za ta ci gaba da tallafawa wannan tsari na karatu daga gida.

Mai dakin gwamnan Legas Joke Sanwo-Olu a ranar Litinin ta wallafa a shafinta na Twitter cewa ta karbi tallafin rediyo. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *