Da Yiyuwar APC Ta Dare Gida Biyu – Tinubu

Kasantuwar samun wadansu matsaloli a cikin jam’iyyar APC, inda har ta kai ga musayan yawu a tsakanin shugabannin Jam’iyyar, wanda hakan ya sa a halin yanzu tafiyar jam’iyyar za ta fara tafiya da murya biyu.

Daga bisani mun samu rahoto inda Bola Tinubu yake ganawa da manema labarai a garin Legas, bayan sun tashi wani zama na gaggawa da wadansu ba’adin ‘kabilar Yarbawa, ciki har da wadansu ba’adin ‘kabilar Hausawa, don cimma matsayar tafiyar jam’iyyar ta APC a kashin nasu tunanin.

Hakan ya ‘kara bude wani sabon fai-fai ne, inda Tinubu yake cewa sune suka yi fadi tashi don ganin an tabbatar da jam’iyyar ta APC, har ta samu karbuwa ga al’ummar Nijeriya’ babu kudanci babu Arewa, kuma farin jinin jam’iyyar APC ta shiga lungu da sako.

Amma duk da haka Tinubu ya yi wadansu kalamai, inda yake nuna alamun zai yi baya-baya da tafiyar ta APC a halin yanzu, nan da wadansu lokaci kadan, don yin nazari tare da wadansu jiga-jigan Jam’iyyar, inda za su fitar da matsayar su a tafiyar.

Kana an samu karin wadansu bayanai inda Tinubu yake cewa dole su yi wa APC kwaskwarima, kodako babu tunanin wadansu masu fada aji a cikin jam’iyyar ta APC, kuma suna da tabbacin idan suka kawo wannan tunanin lallai za a iya samun sauyi na tafiyar ta su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *