Buhari Ya Mayar Da Farashin Man Fetur N143

Buhari ya mayar da farashin man fetur N143
Hukumar Ƙayyade Farashin Albarkatun Man Fetur, PPPRA, ta sanar da sabon farashin man fetur da zai kama daga N140.80 zuwa N143.80 duk lita.

A wata takarda da ta fitar, PPPRA ta shawarci dillalan man fetur da su siyar da man a wannan sabon farashi na N140.80 zuwa N143.80 duk lita a watan Yuli.

“Bayan bitar muhimman abubuwan kasuwa a watan Yuni da kuma duba da kuɗaɗen da dillalai ke kashewa a zahiri, iya abinda zai yiwu, muna son mu bada shawarar sabon farashin man fetur na N140.80 zuwa N143.80 duk lita a watan Yuli, 2020.

“Ana ba dukkan dillalai shawarar yin aiki da farashin da aka nuna kamar yadda PPPRA ta bada shawara”, in ji takardar.

A ranar 31 ga Mayu, 2020, PPPRA ta sanar da sabon farashin man fetur na N121.50 zuwa N123.50 a duk lita.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *