Shawarwari 8 Zuwa Ga ‘Yan Mata

1- Karkiyarda Ki Nunawa Saurayinki Cewa Ke Kin Dogara Ne Dashi, Kullum Kirika Nuna Masa Kafin Yahadu Dake Kina Rayuwarki Kuma Idan Kuka Rabuma Zakici Gaba Da Rayuwa Mai Dadi.

2- karkiyarda Kice Bazakiyi Soyayya Da Talaka Ba Domin Wanda Kike Kallo Talaka Yau Gobe Shine Mai Arziki, Shikuma Mai Kudi Yau Zai Iya Zama Talaka Gobe, Rayuwa Tana Kasancewa Ne Tamkar Fankar Kasa Idan Ta Juya Ta Nan Anjima Can Zata Juya.

3- karkice Samari Na Gaskiya Masu Son Aure Basa Zuwa Wajenki Bayan Komai A Rayuwarki Na Karya Ne. Shigarki, Kalan Jikinki, Yanayin Rayuwarki Da Kuma Shi Kansa Sunanki .

4- karkice Dukkan Mazan Da Suke Zuwa Wajenki Yan Iskane Ba Aurene Yake Kawosu Ba, Karki Manta Yadda Kike Sanya Tufafi Shine Yake Nuna Ke Wacce Irin Macece.

5- Karkice Kunyi Shekara Da Shekaru Kuna Soyayya Amma Har Yanxu Yaki Yarda Kuyi Aure, Yar Uwa Karki Manta Aure Bashine Karshen Soyayyah Ba Kisoshi Tsakaninki Da Allah Shine Zaisa Ya Aureki Ba Dadewa Ba .

6- Karki Tsani Soyayya Saboda Abinda Yafaru Dake A Baya Idan Baki Mantaba Dukkan Abinda Yake Faruwa Damu A Rayuwa Kamar Darasine Yau Mummunan Abu Zai Faru Gobe Kyakyawa Yafaru Don Haka Kiyi Fatan Alkairi Cikin Rayuwa Shine Abinda Ya Dace Dake .

7- Yar”uwa Karkiyi Gaggawan Cewa Sai Kinyi Aure Da Wuri, Karki Manta Allah Shine Yasan Lokacin Da Kikazo Duniya Sannan shi Kadaine Yasan Ranar Mutuwarku Don Haka Idan Lokacin Komai Yazo A Rayuwarki Sai Ya Kasance Kamar Mutuwane Idan Lokaci Yayi Dole A Tafi.

8- Karkice Dukkan Samari Masu Damu Dakeba Bayan Kullum Kina Hanyar Zuwa Hotel Kullum Kina Gaban Motar Samari Keba Makanikiyaba, A Facebook Kinada Abokai Sama Da Dubu 5 A Bbm Kinada Abokai Sama Da Dubu Abar Maganar WhatsApp,2go,Eskimi Da Sauransu Bayan Ke Ba Wata Hamshakiyar Yar Kasuwa Ba.

Yar Uwa Karki Manta Komai A Rayuwa Yana Faruwane Yadda Allah Yakeson Yakasance, Ki Nemi Dacewar Allah a Dukkan Komai Kawai .

Daga: Alhajiji Anas Sales

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *