Ganduje Ya Jagoranci Kona Miyagun Kwayoyi Na Kimanin Miliyan 360 A Kano

Gwamna Ganduje Ya Jagoranci Kona Miyagun Kwayoyi Da Jabun Magunguna Na Kimanin Naira Milyan 360 A Kano

Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje da mataimakin sa Dr Nasiru Yusuf Gawuna sun halarci bikin kona jabun magunguna da kwayoyin shaye-shaye wanda kudin su ya haura naira milyan 360 wanda jami’an tsaro da suka hada da HISBAH, KAROTA da sauran su suka kama, kuma aka kona su a harabar hukumar NDLEA a yau.

Gwamna Ganduje ya jaddada kudurin gwamnatin sa na ganin an shawo kan matsalar shaye shaye a Kano, inda shugaban na NDLEA reshen Kano ya yabawa Gwamna Ganduje bisa yadda yake yaki da miyagun kwawoyi a jihar, inda a yanzu Kano take matsayin ma 6 a jihohin da ake shaye shaye wanda kafin Gwamna Ganduje, jihar Kano ce ta daya shekaru biyar da suka wuce.

Salihu Tanko Yakasai
Special Adviser Media
Government House Kano
June 30, 2020.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *