A Aiwatar Da Hukuncin Kisa Ga Duk Wanda Aka Kama Da Makamai – Tambuwal

Gwamnan jihar Sokoto da ke Najeriya, Aminu Waziri Tambuwal, ya yi kira a rika aiwatar da hukuncin kisa ga duk wanda aka kama ya mallaki makamai ta haramtacciyar hanya.

Gwamna Tambuwal, wanda ya sanar da hakan yayin wani taro a Sokoto ranar Litinin, ya ce ko dai a yi hukuncin kisa ko kuma majalisar dokokin kasar da fadar shugaban kasa su fito da dokar da za ta ba da damar yin hukuncin daurin rai-rai ga masu rike da makaman ba bisa ka’ida ba.

Gwamnan ya ce shirye-shirye sun yi nisa don kafa wata rundunar bijilanti a jihar da nufin magance hare-hare ‘yan fashin daji kan al’ummomin wasu sassa.

Jihar ta Sokoto na cikin jihohin da ‘yan fashin daji suka addaba inda ko a watan jiya sai da suka kashe mutane fiye da 60

BBCHAUSA

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *