‘Yan Sanda Sun Kama Wani Dan Bindiga Dauke Da Bindiga Kirar AK-1”47 A Neja

Jami’an tsaro na ‘yan sanda wadanda suke aiki karkashin rundunar ‘yan sanda reshen jahar Neja sun kama wani Wanda ake zargi Dan bindiga, Ibrahim Mohammed, wanda aka fi sani da suna Shagari A yayin da take dauke da bindiga kirar AK-47.

‘Yan Sanda dake aikin karkashin ofishin ‘yan sanda na Sarkin-Pawa suka cafke shi a yayin da suka tare shi suna bincikar matafiya a bisa kan hanya.

An Gano cewa jami’an sun tsare babur din Shagari ke bisa kai Tare Da wani fasinja inda suka Gano bindiga a yayin da shi abokin Shagarin (fasinja) ya tsare daji a guje.

Bincike ya nuna cewa Shagari ya kasance Daya daga cikin ‘yan bindigar Da suka addabi al’ummar yankin na tsawon Shekara biyu Tare Da Kashe wasu Da cikinsu kafin su sace dukiyarsu

Ya fadawa Jaridar The Punch cewa Yana hanyar shiga daji ne inda sauran yan uwansa yan bindiga suke kafin yan sanda suka ram da shi.

“Ni dan asalin Kauyen Mayigara a Karkashin karamar hukumar Zaria, jahar Kaduna ne. Na San hanyar Minna zuwa Sarkin Pawa ciki da waje domin a nan ne muke gudanar da ayyukar ta’addancin mu. Mu kan yi amfani da dajin ne a matsayin wurin buyar mu kafin mu fita kai hari sannan Mun kasance a wurin na dadewa yanzu,” ya furta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *