Sojin Najeriya Tayi Nasarar Kama Wasu Yan Kasashen Waje A Cikin Barayin Dajin Neja (hotuna)

Rundunar Sojin Najeriya karkashin OPERATION GAMA AIKI: sunkai Hari ta sama a Karamar Hukumar Mariga ta Jahar Niger Inda suka yi Nasarar Fatattakar Barayin tareda Kama wasu Guda Biyu Yan Kasashen Waje.

An Kaddamar da Harin ne a tsakanin Shekaran Jiya 28/06/2020 da Jiya 29/06/2020 a Kauyen Kasuwan Ango dake Karamar Hukumar Mariga ta Jahar Niger Inda Sojojin suka kaima Yan Taaddar Hari tareda Kashe wasu daga cikin su wasu kuma suka Gudu da Harbin Bindinga.

Hakan yasamu Nasara ne Sakamakon Bayanan Sirri da Jami’an tsaron suka samu cewa anga wasu Bakin Mutane cikin Bakaken kaya tareda Shanu da yawa, hakan yasa Rundunar Aikewa da Jirgin Yaki, Wanda yayi ruwan wuta akan Barayin, inda dayawa suka Gudu cikin wadanda suke gudun tsira ne aka kama wasu Yan Kasashen Waje su Biyu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *