Mu Sha Dariya: Sarkin Musu

Wani gwanin musu ne duk inda ya zauna sai ya tada musu. Sai wani yace masa “duk musunka bakakai waneba, ya kira sunan wani wanda yafi wannan shahara a kan musu.

Sai ya ce shi bai yarda akwai wanda yafi shi musu ba, a ina yake? sai ya misalta masa garin da mutumin yake harma da layi da lambar gidansa.shikuwa ya niki gari har gar in yaje kuwa har kofar gidan.

Toh, a lokacin da ya isa dare yayi, mutumin ya rufe kofa, sai ya kwankwasa mutumin ya ce wanene? sai ya ce nin eh!!

Sai maigidan ya ce “a’a ba kaibane yace ni ne , ya ce a’a bakaibane ya ce wallahi ni ne ya ce sam ba kai bane. Haka dai sukayi tayi karshe dai mutumin nan ya hakura ya koma garinsu yana tafe yana cewa lallai yau na gamu da gamona.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *