Kada Ku Dauki Matsalar Shaye-shaye Da Miyagun Kwayoyi A Matsayin Karamin Laifi – Cear Ganduje Ga Al’ummar Kano

Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya kirayi jama’ar jihar da cewa kada su ɗauki matsalar shaye-shaye da safarar miyagun kwayoyi a matsayin ƙaramin laifi, yana mai nuna bukatar samar da wasu hanyoyi da zasu taimaka wajen kawo karshen matsalar.

Ganduje yayi wannan kiran ne a wani sakon ranar yaki da shan miyagun kwayoyi ta duniya wanda ya bayyana ta bakin Kwamishinan yada labarai na jihar Kano Mallam Muhammad Garba.

Ganduje yace wannan rana tana da muhimmanci sosai duba da yadda mutane suke da karamin fahimta kan illar shan miyagun kwayoyi.

Don haka ne Ganduje ya ja hankulan masu ruwa da tsaki a bangaren yaki da miyagun kwayoyi da su cigaba da samar da hanyoyin wayarwa da jama’a kawuna akan illar shan miyagun kwayoyi.

Ya bada shawarar cewa kafafen yada labarai da su kirkiro da hanyoyin fadakar da al’uma kan illolin da miyagun kwayoyi ke haifarwa jama’a a rayuwa harma da tattalin arzikin su.

Ganduje yace tun kafuwar Gwamnatin sa, ta kirkiro hanyoyin yaki da shan miyagun kwayoyi daban-daban wanda harma daga ciki an sami nasarar tarwatsa miyagun kwayoyi wadan da adadin su ya kai na Naira Bilyan Ɗaya.

Sauran kuwa sun hada da kudurorin da Gwamnatin sa take da su na yaki da shan miyagun kwayoyi inda yace gwamnatin sa a yanzu haka tana kokarin kirkiro da hukumar kula da magunguna, wacce zata soma bincikar masu rike da mukaman siyasa da dai sauransu.

Daga bisani Ganduje ya yabawa hukumar UNDP kan zaban jihar Kano da ta zamo cibiyar kafa ofishin ta na shiyar arewa maso gabashin Nijeriya da kuma nadin dan jihar Kano Habeeb Yahaya Hotoro a matsayin jami’in hukumar inda ya danganta yin hakan da la’akari da jihar a matsayin wacce tayi fice a bangaren yaki da shan miyagun kwayoyi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *