Jami’ar BUK Kano Ta Kulla Yarjejeniyar Noma Da Kamfanin Dantata

Kamfanin Dantata ɓangaren dake kula da sarrafa kayayyakin abinci ya ƙulla yarjejeniya aiki tare da cibiyar Nazari da bincike akan harkokin noma a yankuna masu ƙarancin albarkatun ruwa ta Jami’ar Bayero.

Shugaban Jami’ar Bayero ta Kano Farfesa Muhammad Yahuza Bello ne ya sanya hannu akan yarjejeniyar, yayin da shugaban Kamfanin na Dantata Foods Alhaji Tajudeen Aminu Dantata shi ma ya sanya hannu a madadin kamfanin.

Farfesa Jibrin Muhammad Jibrin wanda shi ne Daraktan Cibiyar nazari da bincike kan ayyukan noma a yankuna masu karanci ruwa, wanda ya yi karin haske game da aikace-aikacen cibiyar, ya ce baya ga kamfanin Dantata, suna aiki tare da wasu cibiyoyi da kamfanoni  ciki da wajen ƙasar nan.

Dama dai masu kula da lamura a bangaren aikin noma, na nanata bukatar samar da yanayin haɗaka na aiki tare tsakanin kamfanoni masu sarrafa kayayyakin abinci da kuma cibiyoyin bincike da nazarin dabarun noma a matsayin matakin bunƙasa ƙas da abinci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *