Gwamnatin Tarayya Ta Rage Farashin Lasisin Aure Da Kaso 83 Cikin 100


Gwamnatin tarayya ta amince da rage kudaden da ‘yan Nijeriya ke biya a matsayin lasisin aure a fadin kasar.

Daraktan yada labarai na ma’aikatar harkokin cikin gida, Muhammad Manga ne ya bayyana hakan jiya Litinin a wata sanarwa da ya fitar.

A cewar Manga, ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola ne ya sanar da wannan batu a wata takardar sanarwa ga jama’a wacce ta samu sa hannun sakatariyar dindindin kuma magatakardar harkokin aure ta ma’aikatar harkokin cikin gida, Misis Georgina Ehuriah.

Aregbesola ya ce, hukuncin ya biyo bayan shawarwarin da masu ruwa da tsaki suka bayar ne a waje taron wayar da kai da aka gudanar a rubu’i na uku na shekarar 2019.

Wannan doka ta rage kudin lasisin aure zai fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Yuli, 2020, kuma sabon farshin ya koma N5,000 a shekara a madadin N30,000 a shekara biyu da ake biya a baya.

Sai dai dokar ta ce, mai bukatar lasisin zai biya kudin ne na shekara uku a nan take, sannan in ya zo zai sabinta lasisin, zai sake biyan na wasu shekaru ukun ne.

Haka kuma, domin yi wa lasisin sabon aure inshora, sabon tsarin ya rage kudin inshorar shima daga N30,000 a shekara biyu, zuwa N6,000 a shekara, amma mutum zai biya na wata shekaru biyar nan take, kuma zai ci gaba da sabunta shi da shekara biyar-biyar.

Sannan kuma gwamnati ta rage cajin da ta ke karba ga mutanen da za su yi auren kotu, inda ma’auaratan da ke da bukatar gama garin lasisi za su biya N15,000 a madadin N21,000 da ake biya a baya.

Haka suma ma’auaratna da ke da bukatar lasisin aure na musamman sun samu ragi daga N35,000 zuwa N25,000.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *