Ana Ƙoƙarin Ceto Ran Yaron Da Akayi Wa Yankan Rago A Kano

Wasu marasa imani da ba a san ko su wanene ba sun yi wa wani Yaro yankan rago A unguwar Rijiyar Lemo dake karamar hukumar Fagge a jihar Kano.

Lamarin ya faru ne a daren ranar Lahadin da ta gabata.

Kamar yadda shedun gani da ido suka tabbbatar sun ce sun jiyo yaron yana ihu na a kawo masa dauki yayin da jini yake zuba ajikinsa.

Nan take al’ummar unguwar suka dauke shi zuwa asibitin Aminu Kano domin ceto rayuwarsa.

Shugaban karamar hukumar Fagge Honarabul Shehu Ibrahim ya ce zai dauki nauyin jinyar yaron har ya samu lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *