‘Yan Sanda Sun Kama Shahararren Barawon Mota A Abuja


Jami’an ‘yan sanda sun kama wani barawon mota, Baba Aliyu, wanda ake zargi da satar wata mota kirar Toyota Camry mai dauke da lambar mota RSH 379 AP. 


Shi wanda ake zargi ya zama a Lambata ne dake karkashin karamar hukumar Gurara a jahar Neja inda ya sace motar a Wuse, a birnin tarayya Abuja.


Jami’an ‘yan sanda dake aiki karkashin ofishin ‘yan sanda na Gawu Babangida suka cafke wanda ake zargi da satar motar kirar Toyota Camry bayan sun samu rahoton satar.

Kakakin rundunar, Wasiu Abiodun, ya bayyana hakan a wani sanarwa a ranar Litinin.

”Direban motan ya ki tsayawa a yayin da Jami’an tsaro suka tsaida shi, har ya kai ga Sai da suka bi shi suna tsere Da shi a mota kafin ya yasar da A lambata ya shiga tseree dasu a kafa”

”’Yan Sanda sun bi sahun sa har ya kai ga suka harbe shi a kafa kafin suka samu nasaran cafke shi.”


A nan take ba tare da bata lokaci ba aka garzaya da shi zuwa asibiti domin yi masa magana kafin ca je shi zuw a kotu bayan ‘yan sanda sun gama gudanar da bincikensu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *