‘Yan Bindiga Sun kashe Mutum 11 A Katsina

Duk da Shugaban Sojojin kasan Nijeriya, Janar Tukur Yusuf Buratai, na jihar Katsina domin dakile hare-haren yan bindiga da suka addabi jihar Katsina. A daren jiya ne yan bindigar dauke da manyan makamai suka kai hari a kauyen Bakkai, da ke gundumar Zango ta karamar hukumar Kankara, inda suka kashe mutum tara har lahira kuma ana ana cigaba da neman mutune da dama, wanda har zuwa marecen nan ba’a gansu ba, Kamar yadda majiyar RARIYA ta bayyana.

Wani mazaunin garin, wanda baya so a ambaci sunansa ya shaidawa RARIYA ta waya cewa yan bindigar sun zo garin Bakkai da misalin karfe daya na daren jiya lahadi, inda Suka cigaba da harbe-harben kan mai uwa-da-wabi a garin, inda suka kashe mutum takwas nan take, yanzu haka muna cigaba da neman mutane da dama, da baa ji duriyarsu ba. Kuma sun kwashe dabbobin garin tun daga shanu da tumaki da kuma awakai sun arce da su.

Haka kuma yan bindigar sun kai makamanci wadannan hare-haren a kauyukan Unguwar Madugu da kuma Kauyen Albasun Durumi a Karamar Hukumar Dandume, inda suka kashe mutum daya a koina. Sun sace shanu sama da hamsin.

Majiyar RARIYA ta kara da cewa an yi zanaidar su kamar yadda addinin musulunci ya tanada a garin na Bakkai da marecen yau litinin. Kuma jami’an tsaro sun shigo garin, amma sun fita da marecen nan.

Shugaban Sojojin kasan Nijeriya, ya ce nan gaba kadan zaa murkushe yan bindigar nan, da suka addabi jihar Katsina dama arewa maso yamma. Ya Yi kira ga al’ummar da su ba jami’an tsaro hadin kai da kuma adduar samun nasarar kakkabe su.

Duk kokarin da RARIYA ta yi na jin bakin kakakin Rundunar yansanda ta jihar Katsina, SP Gambo Isah abun ya ci tura.

Daga Jamilu Dabawa, Katsina

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *