Tsohon Ma’aikacin Gwamnati Da Ya Zama Mai Bara Bayan Ya Yi Ritayarsa

Shugaban asusun fensho na jahar Neja, Alh. Sulaiman Annu Kuta (Wakilin raya kasan Minna da Kuta) ya fita ya bar ofishinsa bayan ya samu labarin wani ma’aikacin gwamnatin jahar neja mai ritaya wanda ya koma bara bayan ya makance tun kafin ya samu damar karbar fansho nasa.

Ga yadda labarin ta kasance tsakanin Shugaban asusun hukumar yan fansho na jahar da Tsohon ma’aikacin!!


Shugaban asusun: Assalamualaikum Baba, ina kwana
Baba: waalaikumsalam, lafiya Lau yaro

Shugaban asusun: Baba inada tambaya dana keso namaka


Baba:ina sauraranka

Shugaban asusun:Shin da gaskene kayi aikin gomnati?


Baba:babu shakka yaro, kaga ID card nawa.

A nan take Shugaban ya fashe da kuka ta tambaye ya fadawa mutumin dake rike da takardarsa da kawo takardun nasa zuwa ofishinsa a nan take ba tare da bata lokaci ba.


Babu shakka wannan labarin mai ratsa zuciya ne.

Allah ya biya Alh Suleiman Annu…

Daga Mustafa Anka Kuta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *