Matar Dr. Dre Ta Bukaci Kotu Ta Raba Auren Shekara 24 Dake Tsakaninta Da Mijinta

Matar shahararren furodusar waka sannan mawakin rap, Dr. Dre wacce ake kira da suna Nicole Young, ta mika takardar raba aurenta dake tsakinta da mijinta, Dr. Dre, bayan Shekara 24 da aure.

A cewar takardar aure da aka mikawa kotun County na birnin Los Angeles, Nicole Young, ta bukaci raba auren me sakamakon rashin rashin jituwa dake tsakaninta da mijin.


Wata mijiyar TMZ ta ce Dr. Dre mai Shekara 55 a Duniya Da matarsa, Young, ba su Da wani yarjejeniyar raba arzikinsa da yayi a lokacin da suke tare Idan har za su rabu. Dukiyarsa ya kai kimanin miliyan $800.


Young ta ce ita kawai abunda take bukata shine kudin ciyar Da yaransu da za su kasance hannunta wanda a halin yanzu ta mika takardar neman hakan fa lauyarta, Samantha Spector. Ita karan kanta Young ta kasance lauya ce sannan a baya ta auri shahararren Dan wasan kwando, Sedale Threatt.


Ma’auratan wadannan ke neman a raba auren nasu sun yi aure ne a 25 ga watan Mayu, 1996 sannan suna da yara 2 manya. Da namiji, Truice, da kuma mace, Truly.


Ga baki daya dai, Dr. Dre ya kasance mai yara 6, Hudu maza sannnan biyu mata daga wuraren mata daban har 6. Daya daga cikin dansa, Andre Young Jr. ya rasu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *