Jarumar Nollywood Regina Daniel Tare Da Mijinta Sun Haifa Dansu Na Farko


Jarumar Nollywood, Regina Daniel tare da mijinta, Ned Nwoko, sun haifa dansu na Farko.

Jarumar ta haihu ne a yau Litinin, kwana 2 bayan abokanta sun hada mata bikin gabannin haihuwa wato Baby Shower.

Dan uwan jarumar ya bayyana hakan a shafinsa na Instagram inda ya kara da cewa jarumar ta Haifa da namiji.

Inda ya ruwaito kamar haka;

He said “OFFICIALLY AN UNCLE YOU KNOW?

Wato

“Tabbas Babu Shakka Na Zama Kawu, A Yane?


“Ina ma maki murnar daham dita, an samu da namiji.

“Iyanu ti sele, Gods the greatest.”

wato

“Iyanu ti sele, Allahu Akbar.”


Regina tare da maigidanta sun tabbatar da suna tsammanin haihuwar dansu na farko a watan Mayu.

Jarumar wacce ta aura masoyinta a watan Oktoba ta ce ta aure Dan Shekaru 58 din ne saboda rashin jin ta.

A cewarta, ba za ta girmama wadanda za ta aura da ya kasance tsaranta ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *