Hukuncin Wadanda Suka Yi Zina Kafin Dauren Aurensu


SUNYI ZINA KAFIN AURE
TAMBAYA


Aslm alaikum. Malam Muna Da Tambaya Kamar Haka: Mutum ne Yayi Zina Da Budurwa Kuma Aka Daura Musu Aure Ba Tare Da Tayi Istibra’i ba. Bayan Shekaru Kamar Goma, Sai Suka Fahimci Cewa Zamansu Akwai Matsala. Sai Ya Saketa Ta Koma Gida Don Tayi Istibra’i.


To Tana Gidansu Amma Kullum Yana Zuwa Hira. Kuma Yana Taba Ko’ina A Jikinta Amma Dai Bai Sadu Da Ita Turmi Da Tabarya ba. Data Gama Jini Uku Sai Aka Sake Sabon Aure. Shin Aurensu Na Biyun Ya Halatta?
AMSA


Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Dangane da wannan tambayar akwai mas’aloli da dama.

Da farko dai akwai mas’alar shin auren Mazinaci da mazinaciya ya halatta ne ko bai halatta ba?


Mafiya rinjayen Malamai na Musulunci suna ganin cewa bai halatta adaura aure tsakanin Mazinaci da Mazinaciya ba, har sai bayan sun tuba duk su biyun.


Malaman sun kafa hujjah ne da ayah ta uku acikin Suratun Nuur.


Wasu Malaman kuma ‘yan kadan (Mazhabin Zahiriyyah) sun ganin halaccin haka. Koda ba’ayi Istibra’i ba.


Sun kafa hujjah ne da aikin Sayyiduna Abubakar (ra) azamanin Halifancinsa. An kama wani saurayi da budurwa suna yin zina. Bayan an zartar musu da hukuncin bulala sai Sayyiduna Abubakar ya daura musu aure. (saboda toshe ‘baraka).


Sannan ‘daura aure ba tare da yin Istibra’i ba, shima mas’ala ce wacce Malamai suke ganin cewa auren ma babu shi.


Amma tunda har su da kansu sun rushe auren farkon sun sake yin wani, to wannan na biyun yayi. Kuma wannan kusantar zina da sukayi ba zai hana yiwuwar auren ba. Sai dai kuma laifin yin hakan yana nan akansu sai dai in sun tuba zuwa ga Allah.


Anan nake so in ja hankalin iyaye da masu fa’da-aji, cewa ya kamata arika sabya ido sosai akan abinda ke faruwa acikin unguwanni tsakanin samari da ‘yan mata.
Bai kamata arika zuba ido ana barin abubuwa suna lalacewa haka ba. Ya kamata lallai adena barin Saurayi yana kadaita da budurwa koda ya riga ya biya sadaki. Mutukar dai ba’a riga an daura musu aure ba.
Sannan alkalai da Malamai da Mahukunta ya kamata su rika warware ma mutane hukunce-hukuncen da ya rataya akansu aduk lokacin da wani al’amari irin wannan ya faru.
WALLAHU A’ALAM.
Allah Ne Masani
Bazamfare Ne.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *