Da Dumi-Duminsa: Shugaba Buhari Ya Bude Tafiye-Tafiye Tsakanin Jihohi

Rahoto daga kafafen yada labarai sun bayyana gwamnatin tarayya ta bude tafiye-tafiye tsakanin dukkan jihohi a fadin Nijeriya.

Hakan na zuwa ne a ranar Litinin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya karbi rahoto na biyar daga kwamitinsa na kar-ta-kwana kan yaki da cutar coronavirus, kan halin da ake ciki game da cutar a kasar.

“Ina farin cikin shaida muku cewa Shugaban Kasa… ba amince, sai dai ‘yan sauye-sauyen da za a sanar a nan gaba.

Sai dai ya ce tafiye-tafiyen zasu fara ne daga ranar 1 ga watan Yuli, tsakanin karfe 5 na Asuba zuwa 10 na dare da a baya aka kebance manyan motoci masu dakon kayan abinci da kayan gwari da shi.

Boss Mustapha ya kara da cewa Shugaba Buhari ya amince a bude makarantu ga daliban ‘yan aji shida na firamare, da kuma ‘yan aji uku na karamar sakandare da kuma ‘yan aji uku na babban sakandare da ke shirin jarabawar kammala karatu.

Sai dai ya kara da cewa nan gaba za a sanar da matakan da za a bi wajen bude makarantun.

Ya kuma ce gwamantin ta amince da bude filayen jirgin sama cikin matakan kariyar cutar coronavirus.

Jawabin Boss Mustapha ya ce sassaucin na makonni hudu bai hada da sauran tarukan jama’a a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *