Ban Ce Inyamuri Ba Zai Taba Mulkin Kasar Nan Ba – Yerima

Shugaban kungiyar matasan arewa, Shettima Yerima, ya karyata rahoton da ke yaduwa a kansa mai cewa ya ce inyamuri ba zai taba zama Shugaban kasan Najeriya ba.

Yerima ya bayyana hakan ne a yayin da yake mayarwa tsohon gwamnan jahar Enugu, Dr. Jim Nwobodo, martani inda Tsohon gwamnan ya furta cewa ya kamata a baiwa inyamuri dan kudancin Najeriya kujerar Shugaban kasa.


Duk da haka a yayin da Ake hira da shi a Jaridar Vanguard, Yerima ya ce shi bai furta wadannan kalaman ba. A cewarsa, ya ce wasu yan bata gari ne kawai suka canza masa kalaman da ya furta domin raba kan kasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *