An Yasar Da Gawar ‘Yar Shekaru 6 Da Aka Yi Wa Fyade Har Ta Mutu A Masallaci A Kaduna

An yasar da gawar yarinya mai shekaru shida da haihuwa da aka yi wa fyade har ta mutu a wani masallaci a yankin Kurmin Mashi da ke a karamar hukumar Kaduna ta arewa.

Majiyarmu ta bayyana cewa wannan lamari dai ya faru  e a ranar Juma’ar da ta gabata, inda daruruwan mutane suka bayyana takaicinsu cikin har da kungiyoyin jama’a da suka dunguma zuwa gidansu yarinyar da aka halaka din.

Sai da maus jaje suka yi ban baki ga iyayen yarinyar kafin su amince a kai gawar asibiti domin gudanar da bincike na musamman.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Kaduna, ASP Muhammad Jalige ya tabbatar da faruwar lamarin bayan manaema labarai sun kira shi a waya.

Ya kuma bayyana cewa, zuwa yanzu dai ba a yi nasarar kama ko mutum guda ba da ake zargi da aikata laifin, amma ‘yan sandan ciki na nan na gudanar da aikinsu na sirri don gano wadanda suka aikata wannan mummunan aiki.

Kasancewar ana bude masallacin ne a ranakun Juma’a kadai saboda yanayi na kulle da ake ciki a jihar Kaduna, ya sa mugayen suka faki idanu suka ajiye gawar yarinyar a jikin masallacin da misalin karfe 3:20 na ranar Juma’a, bayan an yi sallah an watse.

Jami’an ‘yan sandan Kurmin Mashi na ci gaba da bincike game da lamarin, kuma za su sanar da zarar sun yi nasarar yin kame.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *