An Gurfanar Da Wani Matashi A Gaban Kotu A Kan Zargi Sata


A ranar Litinin ‘yan sanda suka gurfanar Da wani a matashi Dan Shekara 25, Ogunleye Olarewaju,, a gaban Wata kotun majistare dake Ado-Ekiti a kan zargin Sata


Lauyar da ya mika karar ya bayyana cewa ana zargin matashin Da yin sata a wani gida mara adireshi.

Lauyar da mika karar zuwa kotu, Sifeto Caleb Leramo, ya fadawa kotun cewa wanda ake zargi ya aikata laifin ne a ranar 16 ga watan Fabrairu a Iworoko-Ekiti.

Ya ce wanda ake zargi ya yiwa wani mutum Adeniyi Sodiq sata.

Ya ce wanda ake zargi ya yiwa wanda aka yiwa sata barazanar Aika masa Da kudin da yake bin shi ta waya.


Leramo ya ce hakan ya sabawa sashi 1(1) na dokar Fashi fa makami na Act Cap RII dokar kasar Najeriya, 2004.

Lauyar da ya mika karar ya bukaci kotu da ta daga ranar saurarar karar domin samun damar ci gaba da yin nazari game da abunda ya faru tare da kawo shaidu


Kotun ta yi watsi da wannan bukatar


Lauyar wanda ake zargi, Mr. Ayodele Oguntuase, ya bukaci kotun da ta bada belin wanda ake zargin Da sharadin ba zai karya dokar belin ba.

Alkalin kotun, Cif Majistare , Mr. Abdulhamid Lawal, ya bada belin wanda ake zargi a kan kudi naira N100,000 Da kuma kawo wakilai 2 wadanda za su tsaya mai

Daga nan ya daga saurarar karar zuwa 30 fa watan Yuni.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *