Access Bank Zai Mayarwa Hulda Da Shi Kudin Da Ya Caje Su Na Stamp Duty Bayan Sun Koka

Access Bank ya bayyana cewa zai mayarwa da miliyoyin kwastominsa a fadin Nijeriya kudaden da ya caje su na stamp duty  a tsakanin watannin Fabrairu zuwa Afrilu.

Haka kuma bankin ya yi alkawarin mayarwa da masu hulda da shi kudaden da aka daukar musu daga asusun ajiyarsu a tsakanin Asabar zuwa Lahadi.

Access Bank ya ce, a wata sanarwa da ya fitar, ya fahimci cewa ‘yan Nijeriya na cikin yanayi a wannan lokaci, musamman ma ganin yadda masu hulda da shi suka yi ta kokawa game da cire musu kudin.

Bankin ya bayyana cewa, duk da dai ya zame musu dole su biya wannan caji ga babban bankin Nijeriya, wanda shi ne ya yi umarni ga bankuna da su cire N50 ga a duk wata N10,000 da mutum ya saka a asusunsa.

A saboda haka, kwastomomin bankin Access za su samu jimillar kudaden da bankin ya daukar musu da sunan stamp duty daga watan Fabrairu, 2020 zuwa watan Afrilu, 2020.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *