Yaron Shago Ya Lalata Budurcin Yaran Maigidansa ‘Yan Biyu ‘Yan Shekaru 12

An cafke wani Dan Shekaru 26, Chinedu Obi, a kan zargin lalata budurcin ‘ya’yan magidansa ‘yan biyu mata ‘yan shekaru 12.

A wani sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sanda na jahar Legas ya fitar, Bala Elkana, ya bayyana cewa a ranar 16 ga watan Yuni, Wata mata ta kawo karar wani mai aikin maigidanta Dan Shekaru 26, Chinedu Obi, a ofishin ‘yan sanda dake Aguda a kan zargin lalata budurcin yaranta mata ‘yan biyu a yayin da aka bursu a gida da matashin.

Shi wanda ake zargi an kama shi sannan kuma ya furta laifin Da ake zarginsa da shi. Bala ya bayyana cewa shi wanda ake zargi ya fara saduwa Da yaran ne tun a shekarar 2019.

Sanarwar ta bayyana cewa Kwamishinan ‘Yan Sanda na jahar, CP Hakeem Odumosu, ya bada umurnin mika karar zuwa sashen jinsi dake hedikwatar ‘yan sanda na jahar Wanda Ikeja domin gudanar da cikakken bincike a kan lamarin.

kwamishinan ya ce kada iyayen su rinka yadda da barin ‘ya’yansu da wasu musamman yara mata. Ya kuma kara da cewa rundunar ‘yan sanda tana nan a kan bakanta wajen cafke Duk wadanda aka kama da laifin fyade da makamancinsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *