‘Yan Bindigar Haya Sun Bindige Mutum 2 A Jahar Adamawa


Wasu mutane wadanda ake zargin ‘yan kisan haya ne sun kashe wasu mazauna karamar hukumar Ganye 2 a jahar Adamawa.

An samu labarin hakan ne a ranar Lahadi yayin da ‘yan bindigan suka shiga kauyen Jatau dake karkashin karamar hukumar Ganye a ranar Asabar Da yamma, inda suka gani wasu mutane 2 sannan suka kashe su a lokuta daban daban.

A yayin da ya ke tabbatar mana da faruwan haka, wani mazaunin yankin ya fada mana cewa “wasu mutane 2 a bisa kan babur dauke da makamai suka shigo garin Da misalin karfe 7:00 na yamma.

“Da isan su, suka tambaye inda mutanen da suka zo nema yake da amsarwarsa suka tabbatar cewa shine suka bindiga shi. Sannan hakan kuma ya dake faruwa ga mutumin na biyu Da aka kash.”

Kakakin rundunar ‘yan sanda na jahar Adamawa, DSP Suleiman Nguroje, a ranar Lahadi Da yamma ya ce har yanzu ‘yan sanda na yankin basu yi masa bayani ba a kan lamarin amma hukumomin Garin sun tabbatar da faruwa kashe-kashen Da aka yi.

Ma’aikacin labarai na karamar hukumar Ganye, Kabiru Njidda, ya ce wadanda suka aika kisa ana zargin masu kisan haya ne domin basu Sace komai ba Ko kuma sun yi wani abu Da zai sanya cewa Ko barayi ne face illa kashe wadannnan mutanen biyu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *