Sauke Oshiomole Ba Zai Shafi Yin Takarata Ba – Tinubu

Babban jigo a jam’iyyar APC kuma na hannun daman shugaba Buhari Bola Ahmad Tinubu, ya ce ko kaɗan rikicin da ke addabar jam’iyyar su ba zai shafi batun takarar shi da yake burin yi ba, idan har ya yanke shawarar yin takarar.

Ya ce a halin yanzu ya fi mayar da hankali ne a kan kallubalen tattalin arziki da kasar ke fuskanta a halin yanzu da matsalar annobar coronavirus da mutane ke fuskanta.

A cikin sanarwar da ya fitar a ranar Asabar, a karo na farko, ya yi magana a kan rushe kwamitin gudanarwa ta Adams Oshiomhole na jam’iyyar ta All Progressives Congress (APC).

A ranar Alhamis ne aka rushe NWC din ta Oshiomhole yayin taron Kwamitin Zartarwa, NEC, na gaggawa da aka kira.
Taron ya samu hallarcin Shugaba Buhari, mataimakinsa Osinbajo da wasu jiga-jigan jam’iyyar.

Wasu sun yi wa hakan kallon wata babbar cikas ga shirin takarar shugaban kasa da Tinubu ke da niyyar yi duba da kusancinsa da Oshiomhole. Sai dai sanarwar da jagorar jam’iyyar ya fitar ta nuna cewa ba abinda ke gabansa ba kenan a halin yanzu.

Ya ce, “Ga wadanda suke ta babatun kan yadda matakin da shugaban kasa ya dauka da taron NEC da aka yi ya kawo karshen takarar da na ke niyyar yi a 2023, ina neman suyi min uzuri. “Ni mutum ne kamar kowa kuma bani da wani ilimin gaibu ko ta siyasa da ku ke ikirarin kuna da ita.

Cikin azarbabi, har kun fara kokawa kan niyyar takarar shugabancin kasa a 2023 da ba ta da tushe. “A wannan mawuyacin lokaci da annobar COVID-19 da kallubalen tattalin arzikin da ya jawo ke adabar mu, ba ni da wani hangen nesa da ya fi na ku.

Ban yanke wani shawara ba game da takarar 2023 a halin yanzu, abinda ke gaban mu ya ishe mu. “A wannan lokacin, ba batun siyasar 2023 na ke mayar da hankali na kai ba.

Ina ganin hakan rashin alkibla ne da rashin tausayi duba da irin mawuyacin halin da mutanen mu ke ciki na coronavirus da tattalin arziki. “A cikin watannin da suka gabata, na mayar da hankali na a yanzu kan bullo da tsare-tsaren da za su taimaka wa kasar mu. Lokaci ba yi ba da zan fara maganan abinda zan yi ko ba zan yi ba a shekaru uku masu zuwa.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *