Masari Ya Kai Ziyarar Jaje A Garuwan Da ‘Yan Ta’adda Suka Kai Hare-hare A Katsina

Gwamna Aminu Bello Masari ya kai ziyarar ta’aziyya, jaje da kuma ban hakuri ga al’umomin kananan hukumomin Faskari da Dandume wadanda ‘yan ta’adda suka kai wa hari na babu gaira babu dalili wanda ya yi sanadiyyar mutane sama da Saba’in.

Gwamnan wanda ya fara wannan ziyara da sansanin masu gudun hijira dake a Makarantar Firamare ta Gwaji (Pilot) dake cikin garin Faskari, ya tausaya tare da kuma jajanta wa al’umma baki daya. Ya kuma yi kira gare su da cewa su dauki wannan ibtila’i a matsayin kaddara wadda ba za a iya kauce mawa ba, duk da cewa kuma yin hakan ko kadan ba zai dauke nauyin da ya rataya a kan Shuwagabanni na tsaron lafiyar su da dukiyoyin su ba.

Gwamnan ya bayyana cewa ya san al’umma suna kuka da hawayen su kan wannan al’amari, to amma shi a kullum yana kwana da tashi a cikin tashin hankalin sanin cewa gobe kiyama sai Allah Ya tambaye shi kan wadannan dama sauran al’amurra da suka shafi al’ummar wannan jiha.

Alhaji Aminu Bello Masari ya roki al’umma da suyi hakuri kuma su daure suyi afuwa kan wannan mummunan lamari marar dadi domin Allah na shaida ba rungume hannuwa sukai suna kallo ba, a’a, suna kan kokarin su wadannan matsaloli suke abkuwa.

Gwamna Masari ya kara da cewa kokarin da suke tayi wajen kawo karshen matsala yasa yanzu haka Sojoji sun canza salo da taku na kawo karshen wannan asarar rayuka da dukiyoyi da ake tayi. Haka kuma, rundunat Sojojin kasa ta kasar nan za ta gudanar da bikin ta na shekara shekara a Faskari kuma za su ragade dajin nan kaf din shi domin tabbatar da ba a bar ko da dan ta’adda guda ba wanda zai hana al’umma zaman lafiya.

Ya kuma yi kira ga al’umma da suci gaba da addu’o’in samun zaman lafiya da jagoranci na kwarai daga Shuwagabanni tare kuma da ba jami’an tsaro goyon baya, musamman ta bangaren bada sahihan bayanai da za su taimaka wajen ganowa da durkusar da ‘yan ta’adda.

A nashi jawabin, Sarkin Yamman Katsina Hakimin Faskari, Injiniya Aminu Tukur Sa’idu ya mika godiyar su ga Gwamna Aminu Masari a kan yadda ya nuna kula da damuwa a kan halin da al’ummar wannan yanki suke ciki, ya kuma yi kira ga al’umma baki daya da muji tsoron Allah tare da sauke dukkan nauyin da ya dora mana domin kuwa abin tambayo ne gobe kiyama.

Daga Faskari, Gwamna Aminu Bello Masari ya shiga garin Kadisau domin yin ta’aziyya da jajantawa al’ummar wannan gari inda akayi asarar kusan mutum Saba’in a rana guda. Daga Kadisau sai Dandume a inda Gwamna Aminu Bello Masari ya ziyarci sansanin masu gudun hijira dake Makarantar Firamare ta garin Dandume domin duba halin da suke ciki tare da jajantawa.

A cikin wannan tawaga akwai Maigirma Mataimakin Gwamna Alhaji Mannir Yakubu, Sakataren Gwamnatin Jiha Alhaji Mustapha Muhammad Inuwa, Mataimakin Shugaban Majalisar Dokoki ta jiha Injiniya Shehu Dalhatu Tafoki, Kwamishinan Kula da Muhalli Alhaji Hamza Suleiman Faskari, Mai ba Gwamna Shawara a kan Ilimi Mai Zurfi Kwamared Muhammad Bashir Ruwan Godiya da sauran manyan jami’an Gwamnatin Jiha.

Daga Mainasara Nasarawa Funtua

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *