Ku Dawo Katsina Ku Kafa Kamfanoni – Masari Yayi Kira Ga ‘Yan Asalin Jahar

Masari Ya Yi Kira Ga ‘Yan Asalin Jihar Katsina Da Suke Kasuwanci A Duniya Su Dawo Katsina Su Kafa Kamfanoni, Domin Kawo Karshen Matsalar Tsaron Jihar Katsina

…Dalilin da ya sa muka ba da hayar rumbun ajiyar hatsi da ke Kofar Kwaya na tsawon shekara goma

Daga Jamilu Dabawa, Katsina

Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari ya yi kira da babbar murya ga yan kasuwa, da suke kasuwanci a koina a duk fadin duniya, wadanda kuma yan asalin jihar Katsina da su dawo gida jihar Katsina, domin kafa Kamfanoni da za su samarwa matasa ayyukan yi, wanda zai taimaka matuka wajen kawo karshen matsalar rashin tsaro da jihar Katsina ke fuskanta.

Masari ya bayyana haka, a lokacin da ake kulla yarjejeniyar ba da hayar rumbun ajiyar hatsi da wani Kamfani na Axxon a Ofishin hukumar cigaban kasuwanci ta jihar Katsina, Wanda ya samu wakilcin Mai Baiwa Gwamna Kan Harkokin Noma, Dr. Abba Yakubu Abdullahi.

Gwamnan ya kara da cewa tunda aka yi taron tattalin arzikin na Katsina, mu ke ta kira ga yan kasuwa, yan asalin jihar Katsina, da su dawo su kafa masana’antu, wanda shi zai magance mana matsalar zaman banza da matasan mu ke Yi da Kuma rashin tsaron nan da muke ta fama. Alhamdullih yan asalin jihar Katsina sun fara amsa wannan kira na mu, Shugaban kamfanin Axxon.

Da yake magana kan dalilin ba da hayar rumbun ajiyar hatsin na kofar kwaya, tsawon shekara ashirin da yinsa amma, sau daya aka taba zuba masa hatsi, Mun tattauna yana son bunkasa harkar noman ridi a jihar Katsina, Kuma jihar Katsina ita ce ta biyu a kasar nan a wajen noman ridi. Rumbun nan Yana daukar adadin ton na hatsi, har dubu biyar, da kuma manyan wuraren ajiya hatsi da dama. Shine muka ba shi haya na tsawon shekara goma. Kuma zai kawo injinan sarrafa ridin nan, wanda zaa iya kai shi kasashen waje.

Shima da yake jawabi Shugaban Hukumar Bunkasa Kasuwanci Da Zuba Jari na Jihar Katsina, Alhaji Ibrahim Tukur Jikamshi, Gwamna Masari babbar burinsa ya ga kasuwanci da yan kasuwa sun samu cigaba, shi yasa ya kafa wannan maaikata, domin zakulo masu zuba jari da kuma saukakawa masu zuba jarin a Jahar katsina, idan ya shigo ya ji saukin gudanar da kasuwanci a jihar Katsina. Kuma yin hakan zai samawa dimbin matasanmu ayyukan yi, za kuma a bunkasa harkar noman zamani da kuma maida shi kasuwanci. Matasan mu za su daina kwarara zuwa kudancin kasar nan, zai dawo da su gida, su shiga noman zamani kuma su amfana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *