Ina Matukar Farin Ciki Da Rikicin Jam’iyyar APC, Ina Kuma Addu’ar Allah Ya Sa Ta Ci Gaba Da Hakan – Wike

Gwamnan jahar Ribas, Nyesom Wike, ya ce Yana matukar farin cikin yadda rikici ya barke a jam’iyyar mulki APC sannan kuma Yana mai addu’a Allah ya sa ta ci gaba a hakan.

Wike, wanda ya kasance jigo a Jam’iyyar PDP, ya bayyana hakan ne a yayin da ake hira da shi a Arise TV.

“Ina mai farin Cikin Rikicin da ya barke a jam’iyyar Apc. Ni ba aiki bane hada kan ‘Yan Jam’iyyar APC. Idan za ku iya tunawa Mun taba samun rikici irin haka karkashin Ali Modu Sharrif, ita ma Jam’iyyar APC Ta ji dadin faruwar hakan. Ina mai addu’ar Allah ya sa jam’iyyar ta ci gaba a hakan. Mun samu nasaran karbi Wata jaha. Abun takaici shine jam’iyyar APC ba jam’iyyar siyasa ba ce. Sun hada kai ne kawai don su kwace mulki.

Ni Ina son jam’iyyar ta kasance a bisa kan mulki Saboda haka dole na yi addua Allah ya sa jam’iyyar APC ta ci gaba a haka. Ina so su ci gaba da yi kuskure kullun, sannan kuma jam’iyyar ta ta ci gaba da bunkusa.” Ya ce.

A bangaren kasance Godwin Obaseki a matsayin Dan takarar a gwamnan jahar Edo a Jam’iyyar PDP, Wike ya ce bai da wani matsala game da hakan. Ya ce shi dai kawai abunda ya ke so shine a tafiya da duk mambobin jam’iyyar dake jahar domin su samu nasarar lashe zaben gwamnan jahar a 19 ga watan Satumba 2020

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *