Fyaɗe: A Dandaƙe Mazakutar Duk Wanda Ya Aikata – El Rufa’i

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir el-Rufa’i, ya ce babbar hanyar magance matsalar fyade ita ce yi wa masu aikata laifin dandaƙa.
Malam Nasir ya bayyana hakan ne a wani taro da aka gudanar ta bidiyo ta manhajar Zoom a yau Asabar.
An yi taron ne da nufin lalubo hanyoyin magance matsalar fyade da ta ki ci ta ki cinyewa a kasar.
Gwamnan ya ce cikin harshen Turanci wanda da shi aka gudanar da taron “Remove the tools”, wato a cire kayan aikin.
Sannan gwamnan ya ce a jiharsa ta Kaduna an samu karuwar fyade inda aka yi wa mutum 485 cikin kankanin lokaci a baya-bayan nan, kamar yadda alkaluma suka nuna.