Allah Ya Yiwa Alkalin-Alkalan Jahar Kogi Rasuwa A Inda Aka Killace Masu Korona

An samu rahoton rasuwar Alkalin-Alkalan jahar Kogi, Nasir Ajanah. Rahotanni daga Jaridar TheCable ta ruwaito cewa wani daga cikin iyalan alkalin ya tabbatar da faruwan hakan a safiyar Lahadi, inda ya ce ya rasu ne a inda aka killace masu dauke da cutar korona a Gwagwalada babban birnin tarayya Abuja.


Ajanah ya rasu sati daya bayan rasuwa Ibrahim Shuaibu Atadoga, Shugaban kotun kwastamary

Alkalin ya rasu da shekaru 64 a Duniya sannan ya rike manya manyan mukamai.


An kuma sake samun labarin cewa za a binne shi ne a ranar 28 ga watan Yuni, 2020 a birnin Abuja.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *