Adamawa: Allah Ya Yiwa Sarkin Masarautar Hama Bachama RasuwaAllah ya yiwa, Honest Stephen, sarkin masarautar Bachama Wata Hama Bacahama dake Jahar Adamawa rasuwa.


Basaraken wanda sunansa yake Homun Honest Irmiya Stephen, an haifi shi ne a 6 ga watan Maris 1954.

Kakakin masarautar, Timawus Mathias, ya tabbatarwa manema labarai da labarin hakan.


Ya ce mamacin ya rasu ne da safiyar Lahadi a fadar sa Dake Numan a jahar Adamawa.

“Ya rasu ne bayan rashin lafiya Da ya kama shi. A halin yanzu an fara shirin Byrne shi kamar yadda al’adar Bacahama ta tsara a Lamurde, hedikwatar masarautar.

Mathias ya tuna da ranar da basaraken ya karbi sandar mulki a watan Disamba 15, 2013 daga Tsohon gwamnan jahar, Murtala Nyako.

Marigayi Stephen yayi Rita ya a matsayin ofisar Sojojin Najeriya a 2012 kafin ya karbi sandar mulkin masarautar

Marigayi Tsohon sarkin masarauyar Hama Bachama shine sarki masarautar na 28.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *