‘Yan Kungiyar Sintiri Sun Kashe Wani Matashi A Kan Zargin Satar Waya

Wani yaro dan shekara 17 da haihuwa mai suna Muhammadu Sani Aliyu ya rasu a hannun ‘yan bangar Jan Labule da ke Kofar Doka, Zariya a Jihar Kaduna, bisa zargin satar wayar hannu.

Lamarin da ake zargi ya faru ne a ranar Laraba da rana bayan wani mahauci da ke sayar da nama a garejin da shi Sani da mahaifinsa suke sana’a ya ce wai Sanin ya dauke masa waya.

Bisa wannan koke da shi mahaucin ya yi, sai mahaifin yaron wanda tare suke aiki a garejin ya zaunar da dansa ya bincike shi, amma ya tabbatar masa cewa bai dauki wayar kowa ba.

Duk da haka mahaifin Sani bai gamsu ba, sai ya kira abokinsa Abubakar Umar Dan Bakano dominn ya sake bincikar sa.

Suna cikin haka ne shi mahaucin ya kira ‘yan banga suka tafi da yaron ofishinsu da ke Kofar Doka a cikin Zariya don bincike.

Jim kadan bayan tafiyarsu abokin mahaifin yaron ya bi bayan ‘yan bangar domin ganin halin da ake ciki, amma da kyar suka bari ya gansa, can zuwa yamma aka kira shi aka sanar da shi cewa Sani ya rasu.

Kakakin hukumar’yan sanda na jihar Kaduna ASP Muhammad Jalige ya tabbatar da faruwar lamarin, kuma ya shaidawa manema labarai cewa sun kama shugaban ‘yan bangar  Abubakar Ibrahim tare sa wasu hudu daga cikinsu, kuma yace za a maida su babban ofishin Hedkwatar hukumar domin ci gaba da bincike.

Ita kuwa mahaifiyar yaron mai suna Hannatu ta bayyana cewa sam ba zata hakura da wannan ganganci da aka yi wajen salwantar da rayuwar ɗanta ba, dole ne hukuma ta ɗauki mataki wajen hukunta wanda suka sanadin rasa rayuka ɗanta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *