‘Yan Bindiga Sun Bindige Mutane 3 Tare Da Jikkata Wasu 3 A Katsina

A daren jiya ne, da misalin karfe sha daya, yan bindiga suka kai hari a garin Mara da ke karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina, inda suka kashe mutum Ukku nan take kuma suka jikkata mutum ukku, wanda yanzu haka suna kwance a asibitin garin Danmusa.

Wani Mazaunin garin Mara, wanda ba ya so a ambaci sunan shi, ya shaidawa RARIYA ta waya cewa “Yan bindigar sun shigo da Misalin karfe sha daya na daren jiya, kuma a kafa suka zo. Sun fara harbe-harben kan mai uwa-da-wabi, mutanen gari sun fito tare da taimakon sojoji, aka cinma masu. Amma duk da haka sun kashe mana mutum Ukku, a cikin wadanda suka kashe akwai Aminu Yusuf da Lawal Akushi da kuma Mansir Danliti. Akwai kuma wadanda suka samu raunuka daban daban, cikin su Rabi’u Malam da Shamsu da kuma Sharhabilu, yanzu haka suna kwance a asibitin garin Danmusa. Sun dauki tsawon awa daya ana fafatawa da su.

Tuni dai aka yi jana’izar su kamar yadda addinin musulunci ya tanada a garin Mara na karamar hukumar Danmusa.

Daga Jamilu Dabawa, Katsina

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *