Tonon Asiri: Yadda Ministar Agaji ta warewa ‘yan majalisun tarayya gurbin mutum 50,000 ga shirin N-Power (Hotuna)

An zargi Ministar harkokin Agaji da hidimtawa ‘yan kasa Hajiya Sadiya Umar Faruq ta warewa ‘yan majalisun tarayya da wasu manyan ‘yan siyasar Najeriya gurabe dubu 50,000 daga cikin sabbin ma’aikatan N-Power matasa dubu 400,000 da gwamnatin ta fara dauka.

Wannan zargi ya fito ne daga Jaridar Sahara Reporters wacce ta bayyana cewa, bincikenta ya gano cewa Ministar ta yi haka ne bisa matsin lamba da ta fuskanta daga ‘yan siyasar tun a baya kan shirye-shiryen tallafi da gwamnatin tarayya ta fitar

Majiyar mu ta ce tuni dai wadannan ‘yan siyasar suka buga takardun daukar bayanan mutanen da za su rabawa guraben a mazabunsu, ciki har da Shugaban Majalisar dattijai Ahmed Ibrahim Lawan, Sanata Abdul Ningi, Kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi Abubakar Y. Suleiman.

Ga hotunan a kasa;

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *