Sharri Ko Barazana Baza Su Hanani Aikina Ba – Magu

Mukaddashin shugaban hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), Ibrahim Magu ya ce “babu wani bacin suna da barazana” da za su hana shi yaki da rashawa.

A yayin jawabi ga wakilin kungiyar ‘yan jaridu ta Najeriya a babban birnin tarayya a ranar Alhamis, Magu ya ce dole ne a hana barayi satar arzikin Najeriya.

A wata takarda da hukumar ta fitar, Magu ya ce ‘yan Damfara na amfani da sabon salo wurin yakarsa.

Ya ce, “Masu sata, almubazzaranci da kuma kwashe dukiyarmu ba masoyanmu bane. Dole ne mu dakatar da su. Dole ne mu dakatar da mahandama.

Sai mun dakilesu ta kowacce hanya,” yace. “Yaki da rashawa ba sauki gareshi ba a yanzu kamar a baya. Barayin na amfani da sabbin salo da dabaru wurin doke wasu dokoki da tsare-tsarenmu.

Bayan haka, akwai wasu salon mayar damu baya tare da na dauke mana hankali da suka bullo da shi don ci gaban rashawa. A garemu, ba sabbin salo bane. Muna sane da duk wani kage na ‘yan damfara.

Mun san bata mata suna da suke yi amma ba za mu sare ba. Za mu ci gaba da tona musu asiri tare da fallasa duk wani yunkurinsu na cin amanar kasa.

Ba za mu sare ba!” Ya ce hukumar ta matukar mayar da hankali ta yadda ba za a iya dauke mata hankali ba.

Tsokacin Magu ya zo ne kafin a yi cikakken sati da ministan shari’a Abubakar Malami, kuma Antoni janar din tarayya, ya zargesa da cin hanci.

Ministan ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya saukesa saboda zarginsa da ake yi da waskar da kudaden da ya karbowa, jaridar The Cable ta ruwaito.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *