Mai Unguwa Ya Yiwa Wani Magidanci Dukar Tsiya Hadda Targade A Kano

Ana zargin wani mai Unguwa a garin Rege dake Karamar Hukumar Wudil a jihar Kano me Suna Ibrahim Dan’ibro, da yiwa wani Magidanci cikin Talakawan garin sa duka, magieqncin mai suna Abdulkadir Abdullahi a wani gidan Mai dake bayan gari.

Tun da fari dai anyi zargin cewa mai garin ya sami wannan mutumin a lokacin da yake tsakiyar aiki a gonarsa, sai mai garin ya kira shi zuwa wani gidan Mai dake bayan gari, inda ya lakada masa na Jaki tare da Amfani da Katako wajan dukan nasa gami da raunatashi a hannu, inda yayi masa Targade bayan ya Keta masa riga Dlduk sabida yana neman a bashi gonar su ta Gado da take hannun Me Unguwar.

Magidancin me suna Abdulkadir Abdullahi da muka Iske shi a Ofishin Kare hakkin Dan’adam da jin kai karkashi Alhaji Abdullahi Bello Gadon Kaya, yayin da yake mika kukansa don a kwato masa hakkinsa, shi ne ya bayyana mana hakan.

Ya kuma ce, yadda ya sha na jaki a hannun wancan mai Unguwar, yana kira ga Mahukanta da Masarauta da su kawo musu dauki tare kwato musu Gonarsu domin ba su da karfi sai na Allah.

Shi kuwa Shugaban Hukumar kare hakkin Dan’adam da jin kai Alhaji Bello Abdullahi Gadon Kaya, ya ce za su bincika tare da tabbatar da gaskiya sannan su dauki matakin da ya dace.

Munyi kokarin jin ta bakin wanda ake zargin wato mai Unguwa Ibrahim Dan ibro amma hakan mu ya gaza cimma ruwa, domin ko waya taki shiga amma idan mun same shi zaku ji mu da shi a nan gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *