Ina Mai Gamsuwa Da Salon Mulkin Ka – Cewar Buhari Ga Gwamna Zulum

Mai ba Shugaban kasa shawara kan harkokin saro, Manjo Janar Babagana Monguno ne ya bayyana hakan, a lokacin da ya kai ziyara ga Gwamna Zulum a Maiduguri ranar Alhamis.

Janar Monguno ya kasance a cikin Maiduguri don yin ta’aziyya ga Gwamnati da jama’ar jihar Borno game da mummunan harin da ‘yan kungiyar Boko Haram suka kai a kwanakin baya, inda aka kashe mutane da dama.

Monguno ya samu rakiyar ministan ayyukan jin kai, Sadiya Umar Farouq, Shugaban Hukumar Leken Asiri na kasa, Shugaban kwamiti mai kula da ayyukan soji na majalisar dattijai, Sen. Mohamed Ali Ndume, Shugaban kwamitin majalisar dattijai kan ayyuka na musamman, Sen. Yusuf A. Yusuf, da Shugaban kwamitin majalisar dattijai kan NEDC Hon Hadiza Bukar Abba.

“Ya maigirma Gwamna, Shugaban kasa ya nemi da na zo tare da takwarorina na domin jajantawa tare da yi muku fatan alheri ga jama’ar jihar Borno, kuma in sake tabbatar muku da cewa zai sake sabon shiri wajen shawo kan wannan kalubalen na tsaro” Monguno ya ce.

“Mai Girma Shugaban kasa da kanshi ya yaba maka na kokarin da ka yi a cikin shekara daya daga kasancewa ka Gwamnan Jihar Borno. Yawan kokarin da ka yi wajen shawo kan wannan lamari, ya kasance abin kwarin gwiwa ne ga daukacin al’ummar Jihar Borno. Ka kawo ziyarar mai yawa zuwa Abuja don nemo hanyoyin da Gwamnatin Jihar Borno da hukumomin tsaro za su iya hada hannu, ku yi aiki tare domin magance wadannan miyagu. ” Monguno ya ce.

“Ya maigirma gwamna, mun kuma nuna sha’awar gwamnatin jihar Borno karkashin jagorancinka. Muna son tabbatar muku cewa Mai Shugaban kasa ya umarce mu da mu sake duba dabarun mu da nufin kawo karshen wannan yanayin da mutanenmu a Borno suka tsingi kansu.” Monguno ya ce.

A cikin jawabinta, ministar kula da ayyukan jinkai, Sadiya Umar Farouq ta sanar da gwamna Zulum cewa, wakilan, ban da ta’aziyyar sun kuma ba da tallafin jin kai ga wadanda harin ya ritsa da su, kuma ta kara da cewa an gabatar da motocin masu sa ido ga sojojin da motar daukar marasa lafiya da kayan aikin asibiti ga cibiyoyin kiwon lafiya na tarayya a yankin arewa maso gabas.

Da yake mayar da martani, gwamna Babagana Umara Zulum ya yabawa shugaban kasa Muhammadu Buhari saboda sabunta dabarun yaki da ya yi na kawo karshen tashe tashen hankula a yankin arewa maso gabas.

“A madadin mutanen Borno da kuma gwamnatin jihar Borno, ta nuna matukar godiyarta ga gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari da kuma hakika wannan babbar tawaga, saboda jaje da kuka kawo mana a kan kisan rayukan mutane marasa laifi.”

“Gwamnatin jihar Borno da al’ummar jihar Borno suna cike da farin ciki game da sabon yunƙurin da Shugaban ƙasar ya yi don kawo ƙarshen yan tada kayar baya.” Zulum yace.

“Muna imani da gaskiya cewa wannan gwamnatin za ta yi duk mai yiwuwa don ganin an kawo karshen wannan dabi’ar ta ‘yan ta’adda.” Zulum yace.

Daga Alaji Engr Ibrahim Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *