Gwamnonin PDP 10 Zasu Dawo APC Kwanan Nan – Bello

Gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello, ya ce kimanin gwamnonin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) 10 na hanyar sauya sheka All Progressives Congress (APC).

Ya bayyana hakan ne a hirar da yayi a shirin Politics Today na tashar Channels da yammacin Juma’a.

Yayin da yake amsa tambaya kan shin jam’iyyar APC za ta ruguje idan shugaba Muhammadu Buhari ya fita daga jam’iyyar? Yahaya Bello ya ce hakan ba zai yiwu ba.

Yace: “APC na kara karfi, kuma kamar yadda na fada, za a ga zahirin haka nan da yan kwanaki ko makonni masu zuwa a jihar Edo, Ondo, Anambara, Ekiti da Osun.

Abin takaici ne takwaranmu, dan uwana kuma siriki na, Obaseki ya bar mu, amma a matsayinmu na yan jam’iyya, zamu kwato shi.

Ina mai fada maka cewa akwai kimanin gwamnonin PDP 10 dake shirin shiga APC kuma hakan zai faru nan ba da dadewa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *