Gwamnoni Sun Yiwa Buhari Godiyar Kawo Karshen Rikicin APC

A ranar Juma’a ne, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi wakilcin kungiyar ‘Progressive Governors Forum’ a karkashin gwamna Atiku Bagudu, wanda suka kai masa ziyarar godiya bisa yadda ya kawo karshen rikicin da ke aukuwa a jam’iyyar APC.

Da yake jawabi ga manema labarai a fadar gwamnati a Abuja, jim kadan daga fitowarsu daga zaman sirrin da suka yi da shugaban kasar, Gwamna Bagudu ya ce; ya ce sun kuma yi amfani da wannan dama wajen gabatarwa da shugaban kasar amintattun shugabannin majalisar APC din a karkashin Gwamna Mai Mala Bunin a jihar Yobe.

Daga cikin wadanda suka ziyarci shugaban kasar sun hada da; Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello sai kuma Gwamna Neja, Alhaji Abubakar Bello, gwamnnan Kebbi, Atiku Bagudu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *