Gwamnatin Najeriya ta kasa hukunta jami’an ‘yan sanda na SARS’

Ƙungiyar kare haƙƙin bil adama ta Amensty International ta koka kan cewa har yanzu gwamnatin Najeriya ta kasa ɗaukar mataki kan jami’an rundunar da ke yaƙi da fashi da makami ta ƙasar wato SARS.

A wata sanarwa da ta fitar a ranar Juma’a, ƙungiyar ta ce duk da dokar da aka amince da ita a ƙasar ta hana azabtarwa a 2017, akwai hujjoji da ke nuna cewa har yanzu hukumar ta SARS na azabtar da waɗanda ake zargi da kuma kashe su ba bisa ƙa’ida ba duk da sunan neman bayanai daga wurinsu.

Ƙungiyar ta ce a kalla mutum 82 da biyu jami’an rundunar suka azabtar tare da kashewa tsakanin Janairun 2017 zuwa watan Mayu na 2020.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *