Da Duminta: Mayakan Boko Haram Sun Yi Awon Gaba Da ‘Yan Mata Da Dama

Mayaƙan Boko Haram sun sace aƙalla tarin ‘yan mata da suka kai dozin guda a sabon harin da suka kai a yankin wani ƙauye na jihar Borno.

Rahotanni sun bayyana cewar ‘yan Boko Haram din sun kai hari a daren ranar juma’a da misalin ƙarfe 11 na dare a ƙauyen Malaharam dake ƙaramar hukumar Biu.

Ƙauyen Malaharam yana kusa da garin Damboa kimanin kilomita 87 da Maiduguri babban birnin jihar.

Hakanan ‘Yan ta’addan sun yi awon gaba da kayayyakin abinci da dabbobi bayan lashe kimanin awannin biyu suna aikata ta’asar kamar yadda shaidar gani da ido ya shaidawa jaridar The Sun.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *