Da Duminta: Buhari Shugaba Na Ne, Na Amince Da Wargaza Kwamitin NWC Da Ya Yi


Tsohon Shugaban jam’iyyar APC, Adams Oshiomole, ya ce ya amince da wargaje kwamitin NWC Da Kwamitin zartarwa ta yi a zamanta wanda aka gudanar a ranar Alhamis

Oshiomole a yayin da ya ke magana da manema labarai a ranar Asabar ya ce ya fadawa lauyoyinsa Da su janye karar da suka mika a kansa a gaban kotu.

Tsohon gwamnan jahar Edo ya ce ya daura dammarar kin yarda da hukuncin kotun daukaka kara ta yanke na Dakatar Da shi a matsayin Shugaban jam’iyyar


Ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya taba gayyatarsa Shekaru 2 da suka gabata da ya zo ya gyara jam’iyyar APC sannan kuma tunda Shugaban kasar ya kasance mai hikima ya yarda da wargaza kwamitin ayyukar jam’iyyar ta kasa, dole ya amince da hukuncin da ya yanke domin shi ma shugaba ne a jam’iyyar

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *