COVID-19: Zamu Sake Kulle ‘Yan Najeriya – Gwamnatin Tarayya

Yayin da adadin sabbin mutanen da ke kamuwa da cutar corona ta karu a Nijeriya, kwamitin yaki da cutar ta fadar shugaban kasa ta ce lokaci ya yi da za’a mayar da dokar hana fita.

Za ku tuna cewa lokacin da cutar corona ta barke a Nijeriya, gwamnatin tarayya ta kakaba dokar hana fita a jihohin Legas, Ogun da Abuja na tsawon makonni biyar domin takaita yaduwar cutar.

Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, wanda shine shugaban kwamitin ya bayyana yiwuwar sake sanya dokar jiya yayin hirar kwamitin da manema labarai a Abuja.

Ya nuna bacin ransa yadda ‘yan Nijeriya ke yi wa cutar rikon sakainar kashi.

Ya ce: “Shin kun san gaskiyar magana? Da ina da iko, lokacin mayar da dokar kulle ya yi. Dokar hana fitar ba abu bane da dadi amma lokacin mayarwa ya yi saboda yadda na ga mutane na yi wa abin rikon sakainar kashi”.

Yayin da yake kira ga ‘yan Nijeriya su dau abin da gaske, Boss Mustapha ya cewa mutane su mayar da hankali wajen bin shawari da ka’idojin hukumar.

“Na ga yadda ake wasa da COVID-19 a yau. Mutane na yi kamar abin ta wuce. Wannan ba abin wasa bane kuma ina kira ga yan Najeriya masu sauraron mu cewa; mu dau abin nan da gaske.”

“Kawo yanzu da mutane 500 suka mutu, ba zaka jahilci abin ba, ba zai yiwu kace baka san ko mutum daya da ya kamu da cutar ba.”

Ya ce sun gano har yanzu mutane da dama ba su yarda akwai cutar ba shi ya sa ake kin bin dokoki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *