COVID-19: An Bude Filin Jirgin Nnamdi Azikiwe Dake Abuja Bayan Watanni 3 Da Rufe Ta

An bude filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake birnin tarayya Abuja bayan watanni 3 da rufe ta sakamakon barkewar cutar korona a duk fadin kasar Najeriya.


Mutane masu sufuri Tare Da ma’aikatan filin jirgin sun bi Duk dokokin da aka shirya wajen kare al’umma daga yaduwar cutar

An Gwamnatin Tarayya ta rufe duk filayen jirgin saman dake fadin kasar a watan Maris Domin kokarinta wajen rage yaduwar cutar korona a kasar.‘Yan jarida masu daukar rahotanni tawagar Shugaban kasa ya kafa a kan harkokin da suka shafi Korana sun shiga jirgi daga Abuja zuwa Legas domin gwajin yadda aka shirya tsaro shiga jirgin sama tunda aka rufe filayen jirgin sama.


Ana gwajin cutar korona a duk fasinjoji kafin su hau jirgi a wurin jiran isowar jirage.

Kujerun zama wadanda suka kasance babu tazara a da a yanzu an masu tazara Saboda bin dokar tazara Don kare daga kamuwa daga cutar.

Awaki rubutu a kan kujeru wanda ke bayyanawa fasinjoji a kan kada su yi amfani da wadannan kujeran tare da kuma umurtansu su yi tazara da juna

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *