Buratai Ya Ziyarci Mai Martaba Sarkin Kano (Hotuna)

Maimartaba Sarki Ya karbi Bakunci Babban Hafsan Sojan kasar nan a fadar sa wanda yazo kano ziyarar aiki.

Babban Hafsan Sojan ya bayyana a jawabin sa cewa sunzo Fadar sarkin don Girmamawa da neman albarka da kuma shaida masa muhimman ayyukan da ya kawo su.

A jawabin Sarkin ya Godewa Shugaban rundunar Sojan bisa Wannan ziyara da suka kawo masa ya kuma yaba musu bisa kokarin da suke a Wannan kasa, Maimartaba ya kuma kara yiwa Gen Burtai ta’aziyya ta rashin mahaifiya da yayi a kwanakin baya an kuma yi mata addua ta musamman a karshen ziyarar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *